Daga Aisha Aliyu
Shafukan Sada Zumunta sun Cika da hotunan Jarumar Shirin Izzar so Aisha Najamu Wacce aka fi sani da Hajiya Nafisa da Isa Feroskahn Wanda aka fi sani da Presidor a Cikin Shirin Labarina.
Kadaura24 ta rawaito Aisha Najamu ita da kanta ta wallafa hotunan a Shafin ta na instegram, Wanda Kuma sakin hotunan ya sa mutane suke ta fassara kala-kala.
An dai dauki hotunan Jaruman ne a irin salon nan na hotunan biki kafin aure wato pre wedding pictures a turance .
Al’umma da dama dai Suna ta bayyana cewa hadin Jaruman ya dace ,duk da dai har Yanzu su Jaruman ba Wanda ya fito yace uffan Kan lamari.
Lokaci ne Kadai Zai fayyace Gaskiya abun da aka boye.