Daga Sani Abdullahi Danbala Gwarzo
Babbobi Musamman Dangin su shanu na fuskantar kalubale ya yin da aka debesu daga jihohin Arewa zuwa kasuwannin kudu Musamman jahar lagas.
Dabbobin na fuskantar Kalubalen ne sakamakon irin yadda suke shan wahala kafin su isa daga arewa zuwa kudu, a mafi yawan lokaci dai akan kai dabbobin ne a tsaye wanda hakan yake sawa wasu ke kasa tashi idan sun zauna wasu kuma ke haduwa da karaya ko gocewar Kashi a takaice dai Suna jigata.
Wakilin Kadaura24 ya da ya ziyarci wasu kasuwannin shanu a jahar lagas, ya sami jin ta bakin wani matashi mai suna Naziru Ya’u dake tsaka da tashin wata shaniya, inda ya bayyana dalilan dake sabbaba irin jigatar da dabbobin suke yi jkafin zuwan su kudu daga arewa.
Yace Suna jigata ne sakamakon dauri da tsayiwa ga kuma tafiya mai nisa wanda motar shanun takan iya wuce kwana biyu kafin su karasa Jihar ta Lagos Saboda yanayin Motocin da suke daukar dabbobin.
“Idan mun sami dabbobin da suka jigata sai dai a dauki kurar shanu a dauko su daga mashigar kwata zuwa mayan domin su dabbobin baza su iya takawa da kafafuwansu ba.” Inji Naziru Ya’u
Matashin yace a wasu lokutan ma akan Sami saniyar da ba zata iya ko da yin fitsari ba Saboda da jigata, Inda yace idan suka Sami Waɗanda Suka galabaita to lashakka sai dai kawai a yanka ta.
Irin Wannan nan Matsaloli da dabbobin suke fuskanta babu shakka zasu iya yiwa naman su lahani, Wanda kuma hakan zai iya saukowa har Mutanen da Suka ci naman.
Akwai bukatar dai bukatar masu gudanar da irin wannan sana’ar, su Rika daukar kwararan matakai Waɗanda zasu rika saukakawa dabbobin su rinka isa kudun Cikin hayyacinsu,watakil ko al’umma sa Sami nama mai kyau wanda zai inganta lafiyar su.