Ma’aikatan Kananan Hukumomi sun yi Mana yawa a Katsina – Gwamna Masari

Date:

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya buƙaci shugabannin ƙaramar hukuma da ake shirin zaɓa a jihar da su dage wajen tara kuɗin shiga domin su biya ma’aikatansu albashi “saboda sun yi yawa”.

Masari ya bayyana haka ne ranar Talata yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Katsina, yana mai cewa “albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi ya yi yawa”.

“Game da kuɗaɗen ƙaramar hukuma, gaskiya ne lokacin da muka zo, kusan dukkansu ma’aikatansu sun yi yawa,” a cewarsa.

“Mun yi ƙoƙarin biyansu hannu da hannu don gano haƙiƙanin yawan adadinsu amma duk da haka ba mu iya rage yawan kuɗin da ake biyan su ba a matakin ƙaramar hukuma. Amma kuma dukkansu suna da shaidar ɗaukar aiki ta gaskiya.”

Gwamnan ya ce gwamnatin da ta gabata ce ta dakatar da albashin ma’aikata 2,000.

14 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...