2023: Kungiyar Dalibai ta Kasa ta Nuna Goyon Bayan ta ga Sanata Barau Jibril

Date:

Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) Shiyyar A, ta bayyana goyon bayanta ga shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin na zama gwamnan jihar Kano.
 Shugabannin kungiyar daliban sun bayyana hakan ne a lokacin da suka kai wa Sanata Barau Jibrin ziyarar ban girma a gidansa domin nuna jin dadinsu kan rawar da ya taka wajen aiwatar da ayyuka da dama a manyan makarantun yankin a lokacin da yake shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan TETFUND.
 Da yake jawabi yayin ziyarar, ma’ajin kungiyar wanda ya jagoranci tawagar Kwamared Bashir Sulaiman-Limanchi ya bayyana cewa kungiyar tana alfahari da shi saboda jajircewa da kuma nuna damuwarsa kan ci gaban ilimi a shiyyar Arewaci da ma Nijeriya baki daya.
 ” Sanin kowa ne cewa, ilimi shi ne kashin bayan cigaban dan adam, ci gaban zamantakewa da tattalin arziki, tare da ingantaccen ilimi da aiki a cikin al’umma, tabbas irin wannan al’umma za ta kasance mai wadata kuma abin koyi.”
 “Mun shaida cewa, Sanata Barau Jibrin ya himmatu sosai wajen inganta harkar ilimi da ciyar da al’umma gaba, saboda haka muna alfahari da hada kai da kai, kuma a shirye muke mu hada kai da kai wajen ganin an samu nasarar wannan tafiya ta neman Gwamnan Kano, ” in ji Comrade Limanchi.
 Sai dai ya bayyana cewa bisa la’akari da gudunmawar da Sanata Jibrin yake bayarwa wajen habaka ilimi kungiyar dalibai ta shirya gina filin da ya dace da “Student’s Arena” a Jami’ar Tarayya ta Dutse, jihar Jigawa da za a sanyawa sunan Sanata.
 A cewarsa, sama da dalibai 2,000 sun bada gudummuwarsu ta na Naira 1,000 kowannensu domin gudanar da aikin.
 A nasa Jawabin Sanata Barau Jibrin ya yabawa daliban bisa yadda suka amince da shi, inda ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa Wajen ganin bai ci amanar da dalibai da jama’a suka yi hidimta masa ba Idan Allah ya bashi Kujerar mulki Kano.
 Time Express Nigeria ta rawaito Sanata Barau Jibrin ya yi kira ga daliban da su sake jajircewa wajen ganin sun samu ilimi mai inganci, inda ya ce ilimi a yanzu shi ne makamin da zai iya ceto matasa daga halin ha’ula’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...