Daga Saminu Ibrahim Magashi
Zawiyar malam Bala maiyafe dake unguwar adakawa a jihar kano ta hada gangamin taron yiwa kasa addu’oin neman zaman lafiya, yayin da a gefe guda Kuma zawiyar tayi hubbasa wajan ganin ta shiga sahun masu tallafawa marasa karfi da marayu ta hanyar Samar da Gidauniyar.
Yayin taron addu’ar an yi saukar karatun Ishiriniya, tare da gabatar da makaloli daga bakin malamai da dama, da niyyar jawo hankalin al’umma da kuma kara sanin muhimmancin zaman lafiya da neman ilmin addini da kuma ruko da Zumunci.
Datake bayani Shugabar Gidauniyar Dr Atika Bala Maiyafe, ta bayyan cewa sunyi wannan yunkurine domin zaburar da masu hannu da shuni wajan shirya irin wanann tarurruka domin yiwa qasa addu’a.
Dr. Atika ta kuma kara da cewa lokaci zuwa lokaci za su rika shirya irin Wannan taron addu’ar domin nemawa kasar nan dauwamammen Zaman Lafiya.
Taron dai yasamu halittar dumbin al’umma da suka hada da malam Sheikh Ibrahim Khalil, Sheikh Umar Sani Fagge, da sarkin fawa na jihar kano da dai sauran muhiman mutane.