Gawuna ya rufe kasuwar baje kolin Kano karo na 42

Date:

Daga Zainab Muhd Darmanawa
 Mukaddashin Gwamnan Jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a ranar Asabar din da ta gabata ya bayyana rufe kasuwar baje kolin kasuwanci ta Kano karo na 42 tare da bada tabbacin gwamnati za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro domin ganin Kano ta cigaba zaman lafiya don ta cigaba da zama abar sha’awa ga masu son yin Kasuwanci.
 A cewarsa, gwamnatin Ganduje ta himmatu wajen aiwatar da ababen more rayuwa da za su bunkasa jihar da kuma jawo masu zuba jari.
 “Mun bullo da tsare-tsare tare da aiwatar da sabbin hanyoyin samar da ababen more rayuwa da za su sa Kano ta kayata ta fuskar kasuwanci ga masu zuba jari na kasashen waje da na cikin gida”. Inji Gawuna
 Cikin Wata Sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Mukaddashin Gwamnan Hassan Musa fagge ya Sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24 yace Dr. Gawuna ya umarci ’yan kasuwa da su yi amfani da damar zuba jari a harkar noma ta yadda za a yi amfani da damarsa da kuma dorewar tattalin arziki.
 “A Kano mun baiwa harkar noma fifiko ne biyo bayan kira da goyon bayan da gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta baiwa fannin a wani bangare na kokarin bunkasa tattalin arzikin kasar nan.” Inji shi.
 Don haka Gawuna ya yabawa hukumar KACCIMA bisa yadda ta gudanar da bikin baje kolin kasuwancin tare da ba da tabbacin ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai.
 Da yake jawabi, Shugaban KACCIMA, Alh.Dalhatu Abubakar, ya ce duk da illar COVID-19, bikin baje kolin kasuwanci karo na 42 ya samu fitowar yan Kasuwa daga ciki da wajen kasar nan.
 Ya Kara da cewa ranaku na musamman din da aka ware yayin bikin baje kolin kasuwanci ga Jihohi da Kungiyoyin Kamfanoni, an waresu ne don samar da damar da mahalarta taron zasu nuna kayiyyakinsu, ayyukansu da kuma yin mu’amala da masu ruwa da tsaki da sauran jama’a.
 Bikin baje kolin kasuwanci na Kano karo na 42 dai an fara shi ne ranar 27 ga watan Nuwamba kuma aka kuma rufe a ranar 11 ga watan Disamba 2021 wanda aka gudanar a filin baje kolin kasuwanci dake Kano.

3 COMMENTS

  1. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. מכוני ליווי

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NAHCON ta sanar da ranar da za a fara jigilar Maniyatan Nigeria zuwa kasar Saudiyya

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar kula da aikin hajji ta...

Hisbah ta rushe wajen da aka ce sawun Ma’aiki ya fito a jihar Kano

    Hukumar Hisbah ta kai samame tare da rushe wani...

ƴan siyasa ne su ka kashe Arewacin Nigeria — Inji Gwamna Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ‘yan...

Shugaban Karamar hukumar Bagwai ya kaddamar da aikn gada ta sama da Naira Miliyan 160

Daga Shu'aibu Sani Bagwai   Karamar hukumar Bagwai a jihar Kano...