Inganta Noma: Gwamnatin Jihar Nasarawa ta hada hannu da Kamfanin Silvex International don Samar da Dala Miliyan 60

Date:

Daga Zara Jamil Isa
 Asabar 4 Disamba, 2021
 Gwamnatin jihar Nasarawa ta yi hadin gwiwa da ’yan kasuwa masu zaman kansu a harkar noma don samar da sama da dalar Amurka miliyan sittin domin saka hannun jari kai tsaye a harkar noma da tarawa da sarrafa kayayyakin masarufi a jihar.
  An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne da Kamfanin Silvex International, babban kamfanin kasuwanci a Najeriya, don tafiyar da Kamfanin harkokin noma na Jihar wato Nassarawa Agro-Commodity Company a matsayin kmafani mai zaman kansa da Zai jagoranci Kamfanin tare da kungiyar Vertmance a matsayin reshe na uku za su gudanar da harkokin Kamfanin.
 A karkashin wannan yarjejeniya, jihar za ta mallaki kashi ashirin cikin dari (25%) na hannun jarin kamfanin yayin da Silvex International ke da kashi sittin cikin dari (65%) na hannun jari sai Kuma Kamfanin Vertmance Group da ke da sauran kashi 10% a matsayin Waɗanda zasu yi aiki tare .
 Ana sa ran haɗin gwiwar ta samar da ayyukan yi kai tsaye ga aƙalla Matasa maza da Mata  dubu ɗari da hamsin (150,000) a jihar Nassarawa a sassa daban-daban na sarƙoƙin amfanin gona da suka haɗa da tara amfanin gona da sarrafa su da rarraba kayan abinci da aka gama sarrafa su  .
 Da yake jawabi yayin bikin rattaba hannun, gwamnan jihar Nassarawa Engr.  Abdullahi Sule ya sake jaddada kokarin gwamnatinsa na inganta tattalin arzikin Jihar a fannin noma da kuma kudirin gwamnatinsa na samar da yanayin kasuwanci mai sauki ga masu zuba jari.
 Ya tabbatar wa Kamfanin kudirin jihar na cika dukkan sharuddan yarjejeniya da aka Sanyawa Hannu.
  Shugaban Hukumar Raya Jihar Nassarawa Alh Ibrahim Abdullahi ya kuma jaddada aniyar Gwamnatin Jihar na inganta harkokin noma a Jihar.
 Silvex International Limited ne Zai jagoranci harkokin Aiyuka da Gudanarwar Kamfanin tare da tallafi da Kamfanin Vertmance Group.
  Kamfanin yayi shirin cimma kyakykyawan sakamakon da ake sa ran na gudanar da kamfanin kasuwancin na yau da kullum wanda zai iya yin gogayya da takwarorinsa na duniya tare da aiwatar da ayyukan jihar Nassarawa a matsayin cibiyar kasuwanci ta harkokin Noma ta Najeriya.
 A cewar Alh Abubakar Karfi, Manajan Darakta kuma Shugaban Kamfanin Silvex International, yace gwamnatin jihar Nassarawa ta kudiri aniyar samar da filin Noma mai fadin hekta dubu goma domin tallafa wa fara aikin da kamfanin na Agro-Commodity.
  “Hadin gwiwar an yi ta ne da nufin bunkasa Noman Ridi, gyada, shinkafa, waken soya da citta.  Za mu yi aiki tare da abokan cinikinmu don samar da dalar Amurka miliyan sittin a cikin kankanin lokacin don ganin mun sanya wannan yarjejeniya ta ci gaba da aiki yadda ya kamata.” Inji Abubakar Karfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...