Al’ummar Tsanyawa Sun ce Murtala Garo ya Fitar dasu daga Halin kaka Nikayin Ruwan Sha

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban Karamar Hukumar Tsanyawa Alhaji Kabiru Sulaiman Dumbulun ya yabawa Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo bisa sahallewa da yayi aka gina Rijiyoyin Burtsatse Masu Amfani da hasken Rana Guda biyi da Kuma na tuku-tuka Guda biyu a yankinsa.
Shugaban Karamar Hukumar Tsanyawa Wanda mataimakinsa Alhaji Tijjani Abubakar ‘yan kamaye ya Wakilta ya bayyana hakan ne yayin bikin bude Rijiyoyin Burtsatse a Garin Dumbulun.
Shugaban Karamar Hukumar yace yabon ya Zama wajibi Idan akai la’akari da yadda Aikin Zai taimakawa Rayuwar al’ummar da aka Gudanar musu da aiki, Saboda yadda aikin zai fitar da al’ummar yankin daga halin rashin ruwan Sha.
Yace Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta dauki batun Samar da tsaftataccen Ruwan Sha ga al’umma da muhimmancin, Inda yace hakan ce tasa Karamar Hukumar ta Gudanar da Aikin domin inganta Rayuwar Al’ummar yankin.
Shugaban ya Kara da Cewa an Samar da Rijiyoyin Burtsatse Mai Amfani da hasken Ranar a sakatariyar Karamar Hukumar da Kuma Garin Dumbulum. Yayin da aka Samar da na tuku-tuka a Garin Kabagiwa Gidan Alaramma da Gidan Tuku unguwar Makama dukkanin wuraren yace a baya sun dade Suna fama da Matsalar ta Rashin Ruwa.
A Jawabinsu daban-daban Dagacin Garin Dumbulum Alhaji Nasiru Adamu dana Kabagiwa Malam Umar Zubairu Kabagiwa sun yabawa Majalisar Karamar Hukumar ta Tsanyawa da Kwamishina Murtala Sule Garo bisa Gudunmawar da Suka bayar wajen tabbatuwar Aikin Rijiyoyin Burtsatsen.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tsofaffin Kansiloli Sun Yi Saukar Alƙur’ani da Addu’a na Musamman ga Gwamna Abba

  Ƙungiyar tsofaffin kansiloli na jihar Kano ta gudanar da...

Hisbah ta kama mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama akalla mutane...

Yadda ƴansanda suka kama wasu da suke zargin ƴanbindiga ne a Kano

Rundunar yansanda ta Kasa reshen jihar Kano ta ce...

Rikici a Bebeji: Jigon Kwankwasiyya na zargin an shirya cire sunayen tsoffin kansiloli domin yin kashe-muraba

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar Bebeji...