Yanzu-Yanzu: Gwamnan Ekiti da na Jigawa sun ambaci Ɗanzago da Shugaban APC a Kano

Date:

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Ekiti da na Jigawa sun ambaci Ɗanzago da shugaban APC a Kan

Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, da takwaransa na Jigawa, Abubakar Badaru, sun kira Ahmadu Haruna Zago da shugaban jam’iyar APC a Jihar Kano.

Wannnan al’amari daya faru wata alama ce da za a iya cewa ta faru ta ƙare a shugabancin APC bayan da Fayemi, wanda shine Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, da Badaru, su ka kira Ɗanzago da shugaban jam’iyar APC a Kano.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa gwamnonin, a yau Asabar, yayin jawabin su a wajen taron cikar shekarar Cibiyar Bincike kan Dimokraɗiyya ta Aminu Kano da ke ƙarƙashin Jami’ar Bayero shekaru 21, kowannen su ya kira Ɗanzago da shugaban jam’iyar APC a yayin shimfiɗa a jawaban su.

Jaridar ta ƙara da cewa, wannan shi ne karo na farko da a ka ambata Ɗanzago a matsayin shugaban APC a bainar jama’a, tun bayan da a ka yi zaɓen Shugabannin jam’iyar a Kano.

Tun a lokacin zaɓen shugabannin jam’iya na jiha a ka samu rabuwar APC gida biyu, inda ɓangaren Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, shi kuma tsagin Shekarau ya zaɓi Ɗanzago.

Sai dai kuma, a ranar Talatar da ta gabata ne wata babbar kotu a Abuja ta rushe shugabacin Abdullahi Abbas ta kuma tabbatar da na Ɗanzago a jihar, duk da cewa tsagin Gandujen sun ce za su ɗaukaka ƙara.

23 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...