Daga Abubakar Na’Allah Kura
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Alaramma Ahmed Sulaiman kwamishina na biyu a hukumar kula da makarantun firamare ta jihar Kano.
Gwamnan ya mikawa Shehun Malamin takardar shaidar Kama Aiki ne a Gidan Gwamnatin Jihar Kano a gaban Shugaban Kungiyar Izala na Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sakataren sa Sheikh Kabiru Haruna Gombe.
Kadaura24 ta rawaito Gwamnan ya ce ya nada Malam Ahmad Sulaiman Matsayin Kwamishinan na biyu ne Saboda irin Gudunmawar da ya dade yana bayarwa wajen cigaban ilima da harkokin addinin Musulci a Jihar Kano.
Ya Kuma bukace shi ya zamo Mai cigaba da bada Gudunmawar don inganta harkokin Ilimi a Jihar Kano Kamar yadda Gwamnatinsa ta kudiri aniyar yin hakan.
Malam Ahmad Sulaiman ya roƙi Allah ya sa albarka a kujerar da ya samu da kuma roƙon addu’ar jama’a kan taya sa riƙo.