Da dumi-dumi: Kotu Ta Rushe Shugabancin Abdullahi Abbas

Date:

Daga Munnir Muhd
 Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta soke zaben Shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Kano da bangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gudanar a ranar Talata.
 Alkalin kotun, Mai shari’a Hamza Muazu yace ya amince da zaben da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau suka gudanar.
 Alkalin ya yanke hukuncin cewa bangaren Shekarau mai taken G-7 ya gudanar da zaben wanda kwamitin mutane 7 na APC ya sanya wa hannu.
 POLITICS DIGEST ta ruwaito cewa wadanda suka shigar da kara sun hada da Muntaka Bala Sulaiman da mambobin jam’iyyar 17,980 yayin da wadanda ake karan su ne APC, a matsayin wanda ake kara na daya, Mai Mala Buni, shugaban riko, Sen. John Akpanudoedehe sakataren jam’iyyar na  kasa da kuma Hukumar zabe ta kasa.
 Kotun ta ce duk taron da bangaren Ibrahim Shekarau ya jagoranta sahihine.
 Nuraini Jimoh, SAN shi ne lauyan Masu Kara yayin da Sule Usman, SAN, M.N.  Duru da Mashood Alabelewe Suka kasance Lauyoyin Waɗanda ake Kara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An sanya dokar hana fita a Jigawa

An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare...

Gwamnan Kano ya bayyana abun da gwamnatin za ta yi a filin Idi

  Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar...

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...