Wajibin mu ne mu Taimakawa Makarantun Islamiyya dake Karamar Hukumar Birni – Fa’izu Alfindiki

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Shugaban Makarantar kamaludden Adamu Islamiyya Dr Adam Kamaludden Adamu na ma’aji yace babban Burinsu shi ne samar da  ingantaccen ilimi da Tarbiyya ga mata da matasa.

 Dr. Adam kamaludden Adam na ma’aji ya bayyana hakan ne a yayin bikin saukar karatun Alƙur’ani  Mai girma Karo na shida na dalibai  89 Wanda  ya gudana a farfajir makarantar Dake kusada Asibitin yara na marmara a kwaryar Birni Kano.
  Dr Adam  Yace samar da ingantaccen ilimi shi ne ginshikin cigaban kowacce al’umma adon haka suke bukatar goyan bayan iyaye domin cimma burin da suka Sanya a gaba.
   Dr Adam ya bayyana godiyarsa ga Mai martaba sarkin Kano  Alh Aminu Ado bayero  bisa damar da ya samu na halarta bikin saukar karatun duba dabirin dumbin ayyukan da suke gabansa haka zaluka shugaban ya yabawa            shugaban l karamar hukumar Birni faizu Alfindiki bisa gudunmawar da yake baiwa makaranatar.
A Jawabinsa Shugaban Karamar Hukumar Birni Fa’izu Alfindiki yayi  alkawarin samarwa Makarantar gida domin fadada makaranatar don Kara inganta harkokin Ilimi addini Musulci a yankin.
Ya Kuma bukaci Iyayen Yara da su Kara dage damtse wajen tura ‘ya’yansu Makaranta tare da bibiyarsu , Inda Kuma ya bukaci Daliban da sukai saukar dasu dage da Neman Ilimi addini a fannoni daban-daban domin inganta Rayuwar su.
Shugaban Karamar Hukumar yace Karamar Hukumar ba zata yi Kasa a gwiwa ba Wajen cigaba da taimakawa makarantun Islamiyya dake Yankin domin samun Yara Masu Ilimi addini da Kuma tarbiyya.
 wakilin Kadaura24 Kamal Yakubu Ali ya rawaito mana Cewa Gidan da Shugaban Karamar Hukumar yayi alkawari Zai siyawa Makamai gida ne Mai hawa biyu Wanda Kuma Zai taimaka wajen habbaka harkokin Ilimi a Yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...