Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa
Gwamnatin jihar Kaduna ta dage dakatarwar da ta yiwa Hanyoyin sadarwa Wanda aka dakatar na tsawon watanni uku sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga suke kaiwa Wasu sassan Jihar Kaduna.
Gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida Samuel Aruwan, wanda ya sanar da hakan a ranar Juma’a, ya ce an umarci hukumar da ta dace da harkokin sadarwa da ta dage dakatarwa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Saboda bukatar hukumomin tsaro gwamnatin jihar ta umurci hukumar sadarwa ta kasa (NCC) da ta rufe harkokin sadarwa a wasu kananan hukumomin jihar.
Sai dai Rahotanni sun ruwaito cewa an samu karuwar ‘yan fashi da makami musamman a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin da aka dakatar da hanyoyin sadarwar.
Aruwan ya ce sauran matakai kamar dokar hana babura, hana kasuwannin mako-mako, sayar da man fetur a cikin jarakuna na ci gaba da aiki.