Daga Khadija Abdullahi
Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Mika Sakon ta’aziyyarsa ga kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Murtala Sule Garo bisa rasuwar kanwar Mahaifinsa Hajiya Hadiza Galadima Abubakar.
Cikin Wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Gwamnan Malam Abba Anwar ya aikowa Kadaura24 yace Rashin Hajiya Hadizan Babban rashi ne ga al’ummar Jihar Kano.
Gwamna Ganduje ya bayyana cewa “Don haka ina mika wannan ta’aziyya ga kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Murtala Sule Garo, da daukacin iyalanta, da al’ummar garin Garo da karamar hukumar Kabo, a madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano.
Ya kuma addu’ar Allah ya gafarta, Sannan ya bukaci ‘yan uwa da su Kara Hakurin rashinta.