Yan sanda a Kano sun ce sun gano gawar mutane biyu a kurar bayan wata motar kirar Siena a kan hanyar zuwa Katsina.
Kano Fucus ta rawaito rahotonnin sun nuna cewa binciken ya gano sunan mutumin da ya mutu a Matsayin Steven Ayika yayin da macen aka bayyana sunan ta a Matsayin Chiamaka Emmanuel dukkanin su mazauna unguwar Jaba ne dake nan Kano.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Alhamis, ya ce: “A ranar 23/11/2021 da misalin karfe 0450 na safe, an samu rahoton cewa an ga wata mota a kan hanyar Katsina, dake karamar hukumar Fagge ta jihar Kano dauke da mutane biyu (2) a ciki, namiji daya Mace daya.
“Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, ya taso tare da umurci tawagar ‘yan sanda da su wuce wurin da lamarin ya faru.
“Nan take tawagar ta garzaya wurin da lamarin ya faru. An kwashe gawawwakin, inda aka garzaya da su Asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano, yayin wani Likitan lafiya ya tabbatar da mutuwarsu.