Bincike : Nigeria na Cikin Kasashen da ake Gallazawa Yara – UNICEF

Date:

Wani rahoto ya ce a cikin shekara biyar, ƙananan yara fiye da dubu 21 ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta tantance an ɗauke su aiki a matsayin mayaƙa a yankunan Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya.

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bankaɗo cewa daga shekara ta 2016, yankin Afirka ta Yamma da na Tsakiya sun sha samun adadi mafi yawa na rahotannin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tantance kan gagarumin take haƙƙin ƙananan yara a lokacin rikice-rikice.

Rahoton na UNICEF ya zargi dakarun tsaro da ƙungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai da ci da gumin ƙananan yara a yankunan biyu.

Asusun UNICEF ya ce bayan ƙananan yara sama da dubu 21 da aka ɗauka a matsayin mayaƙa akwai kuma ƙananan yara fiye da 2, 200 da aka yi wa cin zarafin lalata.

An kuma sace ƙananan yara sama da 3,500, sannan an kai hari 1, 500 kan makarantu da asibitoci a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya a cikin shekara biyar ɗin da ta wuce.

Rahoton ya ce a Najeriya an kai hare-hare guda 25 kan makarantu zuwa yanzu, inda aka sace ɗalibai fiye da 1,400.

A cewar rahoton wani rikici da ya yi ƙamari a arewa maso gabashin Najeriya tsawon shekara 12 yanzu, ya zama sanadin kashe dubban yara da nakasa wasu da sacewa da raba wasu da gidajen iyayensu, baya ga waɗanda aka keta wa haƙƙi.

UNICEF ya ce tun shekara ta 2005, duk ɗaya a cikin huɗu na wani gagarumin take haƙƙin ƙananan yara da aka samu a duniya, an aikata shi ne a yankin Afirka ta Yamma ko kuma Afirka ta Tsakiya.

Rahoton ya ce a bara kawai, ƙananan yara sama da 6, 400 ne a cikinsu kuma kashi 32 cikin dari ‘yan mata ne aka keta wa haƙƙi a yankunan na Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...