Daga Maryam Adamu Mustapha
Ministar Kuɗi ta Najeriya Zainab Ahmed ta ce masu fasa ƙwauri ko kuma sumoga ne ke jawo tashin farashin shinkafa a kasuwannin ƙasar.
Da take magana a shirin Politics Today na Channels TV ranar Alhamis, ministar ta ce ‘yan sumoga ne ke cutar da ‘yan ƙasa ta hanyar shigo da kayan da ba su da inganci.
“Kwarai da gaske akwai matsaloli kuma suna tasowa ne saboda fasa ƙwaurin kayayyaki zuwa cikin ƙasa,” in ji ta.
“Akwai ‘yan ƙasa marasa kishi da ke shigo da shinkafa maras inganci, wata ma bai kamata ɗan Adam ya ci ba, amma haka za su kawo ta kasuwa.”
Ministar ta jaddada cewa akwai rundunonin haɗin gwiwa da gwamnati ta samar don yaƙi da fasa ƙwauri “da kuma daƙile ayyukan masu kawo wa tattalin arzikin ƙasa cikas”.
Gwamnatin Najeriya ta haramta shigar da shinkafa ƙasar daga ƙasashen waje da zummar haɓaka nomanta a ƙasar.
Karyakake maciya amana daga neman halak da taimakon Alumma azzalimai