Daga Abdulrasheed B Imam
Karamar Hukumar Kumbotso a nan kano ta tashe zunzurun kudi kusan Naira milyan 15 domin samar da kayyakin koyo da koyarwa da kuma kayan makaranta ga Daliban makarantun firaimare Guda 55 a yankin.
shugaban karamar Hukumar, Alhaji Hassan Garba Farawa, shine ya tabbatar da haka, yayin kaddamar da Rabon kayyakin, yana mai cewa an zabi makarantu Guda Biyar daga dukkannin mazabun karamar Hukumar ta Kumbotso, yayinda aka Raba littattafan karatu dana Rubutu da kayan makaranta ga Dalibai maza da mata domin tallafawa yunkurin Gwamnatin jiha na samar da Ilimi kyauta kuma wajibi.
Wannan na kunshe Cikin wani sako da Mai taimakamasa kan harkokin yada labarai Shazali farawa ya sanyawa Hannu.
kazalika Farawa yace yanzu haka karamar Hukumar ta sayi fili da kudinsa ya kai Naira milyan 20 inda zata kashe Naira milyan 52 wajen Gina makaranta ta zamani a yankin karamar Hukumar, Bugu da kari shugaban karamar Hukumar Alhaji Hassan Garba Farawa yace karamar Hukumar ta samar da tallafin karatu ga Dalibai domin yin karatu a jami’ar Istiqama dake Garin sumaila, awani banagare na yunkurinta wajen inganta harkokin Ilimi a jihar nan.
Wasu daga cikin shuwagabannin makarantun da suka amfana da Tallafin , sun yabawa yunkurin Shugaban karamar Hukumar, sun kuma bada tabbacin zasu Raba kayyakin yadda yakamata.