Ra’ayin Comrede Al-Amin Albarra.
Alkaluma sun nuna cewa zaban shugabancin APC, da akayi 16/10/2021 haramtacce ne.
Aranar 16/10/2021, jihohi goma shadaya 11 suka gudanar da zabukan shugabancin APC bi-biyu jihar Kwara ma da jihar Akwa ibom, ma sunyi nasu zaban har guda uku-uku koma fiye da haka.
To alkaluma sun nuna cewa da wanda suka yi zabe guda bi-biyu ko sama hakan da kuma jihohin da suka zabi mutun daya a matsayin shugaban jam’iyar APC na jiha to wannan shugaban haramtacce ne.
Kuma Shugabancin harma da na mazabu, kananan Hukomomi dama wanda akayi din na 16 ga watan Nuwamba 2021 almatsayin na jihohi alkaluma sun nuna cewa harmtacce ne.
Saboda hujjoji da dalilai kamar haka :
Farko dai kundin tsarin mulkin jam’iyar su na Apc sahi na 3/14 da Kuma kundin starin mulkin Nigeria sashi na 183 sun yi tanadin cewa idan mutum yana da mukami na nadi ko kuma zababban mukami to kuma haramun ne ya rike mukami a jam’iya, wanda kuma ahalin yanzu kowa ya san Mai Mala Buni, shi zabban Gwamnan jihar Yobe, ne amma yake shugabantar apc a yanzu.
Hasalima fa ya hau kujerar shugaban cin Apc ne ta haramtacciyar hanya shi Mai Mala Bunu, saboda sashi na 40 karamun sashi na 2 +3 ackin article 11, na kundin tsarin mulkin Apc, ya shardanta cewa idan aka samu rashin shugaban Apc na kasa ya rasu, Likafarsa ta cigaba, ya sauka bisa radin kansa kokuma an tubeshi daga shugabancin jam’iyar na kasa kamar yadda tafaru da Adam Oshomule, to abunda dokar sashi na 40 kara mun sashi na biyu yace dole ne daya daga cikin mataimakan shugaban apc na kasa wanda yake shiyya daya da shugaba maibarin gado ya hau shugaban cin jam’iyar amatakin na kasa.
Kuma a wannan lokacin wanda yake da wannan damar shine Mista Otunba Niyiyi Adebayo, domun shine mataimakin shugaban Apc na kasa daga Kudu maso kudu, amma alokacin bayanan shugaban kasa Buhari, ya na dashi amatsayin Ministan ma’aikatar Masana’antu da zuba jari takasa, saboda haka atandin sashi na 40 kara mun sashi na biyu na 2+3 acikin article 11 na kundin tsarin mulkin jam’iyar su ta Apc yace anemo mai mukami na gaba, mai mukami na gaba shine maga takardar jam’iyar apc na kasa, shi ne Maimala Bunu, alokacin kuma shima ba ya nan likafarsa ta cigaba ya zama Gwamna jihar Yobe, saboda haka kaitsaye sai anemo mataimakin magatakardar apc na kasa Mista Victor Gyaidam, adoka shine zai hau shugaban cin jam’iyar kuma haka akayi yaje Kotu ya samu fassarar wadancan dokokin da muka kawo daga babbar Kotun taraiyya mai lamba 33 mai dauke da umarni mai lamba FCT/ HC/M/6447/2020. karkashin jagoranacin mai shari’a U.S Bature, wanda kotun ta halarta masa ya gaji Adam Oshemole, amatsayin shugaban Apc nakasa.
Amma abin mamaki sai aka samu wasu daga jihar Revers suka ce sun tube Mista Victor daga shugabantar APC bisa san zuciya, sai aka dora Ajimobi Abiyola, abmatsayin shugaban APC na kasa bisa haram ci, saboda
Shi Mai Mala Bunu da Ajimobi Abiyola, basa cikin wanda suka halarta su jagoranci APC.
Abin da ya haramta Ajimobi Abiyola shi ne shi baya cikin wanda aka zaba a babban taron APC na kasa wanda akayi a 2018, shi kuma Maimala Gwamna ne na jihar Yobe, a halin yanzu saboda haka shugabantar APC da yake yi haramun ne dan haka duk zabukan da aka yi na shugabancin APC karkashin sa shida babu duk daya ne domin an yi shi ne karakashin Maimala, shikuma haramun yake kai ga sashika mun kawo.
Kai idan ma a kaci gaba da tafiya abhaka APC bata yi hallastaccen shugabanci ba to alkaluma sun nuna cewa za suyi asarar zaban duk gari na 2023 irin yadda ta faru da su a jihar Zamfara, 2019.
Saboda haka kada giyar mulki tasa su ki gyarawa, idan fa akayi abunda ake so to tabbas za’aga abunda ba’aso.
Watakila masu karatu zasu ce ai Kotun koli tace zasu iya yin hakan, a cewar Alkali Emmanuel Agim, am adadin alkalai uku daga cikin alkalai bakwai na Kotun Koli.
A fahimta cewa zasu iya yayi tunda jam’iyar su ce, hakan ba yana nufin idan aka kaimata ba zata iya rushe wannan haramtaccen shugabancin ba, kai kowacce babbar Kotun tarayya ko ta daukaka kara zata iya rushe wannan shugabancin na APC domun baya bisa ka’ida.
Matsawar aka samu wasu daga cikin mambobin APC suka kai kara a kan wannan zabukan to alkaluma sun nuna cewa kotu zata iya rushe wannan zaban,Wannan itace gaskiyar magana.
payday childporn tube hello administrator