Daga Kamal Yakubu Ali
shugaban kungiyar Daneji Amintacciyya Alhaji Salisu Mai Manja ya bayyana ingantaccen Ilimi da Cewa shi ne hanya daya tilo da za’a bi domin Magance Matsalolin da al’umma suke fuskanta.
Alhaji Salisu Mai Manja ya bayyana hakan ne yayin bikin karrama wasu manya mutane wadanda suke bada gudunmawa wajan bunkasa harkokin ilimi da rayuwar al’ummar dake yankin unguwannin marmara Daneji, kwalwa da mandawari.
Alh salisu mai manja yace ya zama wajibi ga iyaye su hada hannu da masu kishi dake cikin al’umma domin samarda ingantaccen ilimi ga ‘ya’yansu.
Anasa jawabin shugaban kungiyar alkalami yafi takobi Malam Nazir Musa Shehu yace sun zabo Mutanen da suka karrama ne duba irin gudunmawar da suke bayarwa wajan tallafawa masu karamin karfi dake cikin al’umma .
Mutanen aka karrama sun hadarda Malam Abdullah Daneji, Alh Muntari na Wali, Alh Hamisu Jingau Sai masu Unguwanin Marmara, kwalwa, Mandawari da kuma Daneji.
Wakilin Kadaura24 Kamal yakubu Ali ya bamu labarin cewa taron ya samu halarta al’umma da dama a fadin Jihar Kano.