Kungiyar Daneji Amintacciya ta karrama Wasu Masu tallafawa Ilimi a Kano

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

shugaban kungiyar Daneji Amintacciyya Alhaji Salisu Mai Manja ya bayyana ingantaccen Ilimi da Cewa shi ne hanya daya tilo da za’a bi domin Magance Matsalolin da al’umma suke fuskanta.
Alhaji Salisu Mai Manja ya bayyana hakan ne yayin bikin karrama wasu manya mutane wadanda suke bada gudunmawa wajan bunkasa harkokin ilimi da rayuwar al’ummar dake yankin unguwannin marmara Daneji, kwalwa da mandawari.
Alh salisu mai manja yace ya zama wajibi ga iyaye su hada hannu da masu kishi dake cikin al’umma domin samarda ingantaccen ilimi ga ‘ya’yansu.
Anasa jawabin shugaban kungiyar alkalami yafi takobi  Malam Nazir Musa Shehu yace sun zabo Mutanen da suka karrama ne duba irin gudunmawar da suke bayarwa wajan tallafawa masu karamin karfi dake cikin al’umma .
Mutanen  aka karrama sun hadarda Malam Abdullah Daneji, Alh Muntari na Wali, Alh Hamisu Jingau Sai masu Unguwanin Marmara, kwalwa, Mandawari da kuma Daneji.
 Wakilin Kadaura24 Kamal yakubu Ali ya bamu labarin cewa taron ya samu halarta al’umma da dama a fadin Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...

Sarkin Yaƙin Garko, ya ɗauki nauyin dubawa da raba magunguna kyauta ga marasa lafiyar 1400 a Garko

  Sarkin Yaƙin Garko, mai kishin al'umma, kuma ɗan jam'iyyar...

NAHCON ta yi jigilar Maniyatan Nigeria Sama da 24,000 zuwa Saudiyya a kwanaki 10

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar Kula da aikin hajji ta...