Guda daga cikin ‘yan kwamatin riko na uwar jam’iyyar APC ta kasa, kuma shugaban matasa na kasa Isma’il Ahmad ya bayyana cewar har yanzu uwar jam’iyyar APC ta kasa bata kai ga ayyana waye sahihin shugaban jam’iyyar a Kano ba.
Isma’il Ahmad ya bayyana hakan ne a Wata Zantawa da sukai da gidan Rediyo Freedom dake Kano, inda yace uwar jam’iyyar zata yi nazari sannan ta fadi matsayarta akan shugabancin jam’iyyar reshen jihar Kano.
A karshen makon jiya ne dai aka samu bangarori guda biyu masu hamayya da juna na ikirarin sune halastattun shugabannin jam’iyyar bayan da kowanne yake ikirarin an zabe shi tsakanin bangaren Abdullahi Abbas dake tare da Gwamnatin Kano, da kuma bangaren Danzago da suke tare da Sanata Ibrahim Shekarau.