Majalisa ta hana Ganduje Gina shaguna a masallacin fagge

Date:

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar da ta dakatar da gina shagunan kasuwanci a Masallacin Juma’a na Fagge da ke kwaryar birnin jihar.

Kakakin Majalisa Hamisu Ibrahim Chidari ne ya bayar da umarnin yayin zaman majalisar na ranar Talata, inda ya ce sun kafa kwamati domin bincike kan shagunan da ake ginawa.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa Abdu Madari ya faɗa wa BBC Hausa cewa sun ɗauki matakin ne biyo bayan zargin da ake yi na almundahanar kuɗi.

“A matsayinmu na ‘yan majalisa mun dakatar da ginawa ko kuma sayar da wani fili daga cikin farfajiyar Masallacin Juma’a na Fagge har sai mun kammala bincike,” a cewar shugaban masu rinjayen.

Dan majalisa mai wakiltar karamar Hukumar Bunkure, Muhammad Uba Gurjiya, shi ne zai jagoranci kwamatin na mutum takwas, wanda ake sa ran zai gabatar da rahotonsa cikin mako biyu.

Lamarin na faruwa ne kwana daya bayan Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya sauka daga muƙaminsa a kwamatin Masallacin Fagge saboda zargin badaƙalar da ke cikin aikin gina shagunan.

A baya-bayan nan gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje na gina sabbin shagunan kasuwanci a wurare daban-daban da ke tsakiyar birnin Kano, abin da ke jawo cecekuce tsakanin jama’ar gari.

26 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...