Bayan labarin Kama Matar Ganduje, Gwamnatin Kano ta Karyata labarin

Date:

Daga Nura Abubakar

Gwamnatin jihar Kano ta karyata labarin da ke Cewa an Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta Kama matar gwamnan, Farfesa Hafsat Ganduje.

Sanarwar da kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya aikowa Kadaura24 ya nuna takaicinsa game da labarin Inda yace labarin bashi da tushe ballantana makama.

Ya yi nuni da cewa abin takaici shine, ana yada labaran karya a kafafen sada zumunta ba tare da tabbatar da Gaskiyar labarin daga gwamnati ko EFCC ba.

Malam Garba ya ce ba a kama matar gwamnan ko tsare taba kuma a halin yanzu tana gida Kuma tana kokarin Sauke nauyin da ke kanta.

Tun da sanyin safiyar Wannan rana ne labari ya karade Kafafen yada labarai Cewa Hukumar EFCC ta cafke Hafsat Ganduje, uwargidan gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje kan zargin cin hanci da rashawa da danta ya yi kararta kamar yadda PREMIUM TIMES ta rawaito.

Kamun ya zo makonni bayan kin amsa gayyatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa tayi mata.

Tun da farko an gayyaci Uwar Gidan Ganduje zuwa hedikwatar EFCC a Abuja a ranar 13 ga Satumba, kamar yadda PREMIUM TIMES ta ruwaito a baya. Amma ba ta bayyana ba, sannan EFCC ta yi barazanar kama ta. Majiyoyin da ke kusa da ita daga baya sun ce ta yi balaguro zuwa Burtaniya a lokacin don halartar bikin kammala karatun ɗanta.

Masu binciken suna yiwa Hafsat Ganduje tambayoyi ne kan zarge -zargen da suka shafi badakalar filaye a cikin karar da danta, Abdualzeez Ganduje ya shigar.

Wani mutum, wanda ke da masaniyar kamun amma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce “an kama ta da yammacin Ranar Litinin din data gabata.”

13 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...