Muna tallafawa Mata da Marayu ne don inganta Rayuwar su – Baba Yawale

Date:

Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa

Gidauniyar tallafawa mata da marayu da koyar da sana’o’i, mai suna (Orphans and women support initiative) ta gudanar da bikin yaye matan da suka sami damar koyon sana’o’i daban-daban su kimanin 385 a dakin taro na mumbayya dake nan Kano.

Da yake Zantawa da wakilin Kadaura24 Shugaban Gidauniyar na Kasa Hon. Abubakar Baba Yawale yace Gidauniyar tana gudanar da aikinta don tallafawa Rayuwa marayu da Masu karamin karfi.

Baba Yawale yace sun dawa daga Cikin Matan da aka koyawa sana’o’in Zawara ne, Kuma an yi hakan ne domin su dogara da kawunansu ba sai sun nemi Wani Abu a wajen wani ba.

” Kun San Yanzu hankalin da ake Cikin Wasu Mutanen basa taimakon Mata Saboda Allah sai sun bukaci wani Abu daga garesu Wanda Kuma hakan ba dai-dai bane , to shi yasa muke son matan su dogara da kawunansu ba Sai sun nemi taimakon kowa ba , ballantana a nemi lalata dasu.” Inji Baba Yawale

Yace sun fuskanci kalubale mai tarin yawa Saboda basu ce zasu karbi ko sisin kowa ba, Amma dai yace daga Karshe sun Sami Nasara Kuma Suna fatan cigaba da gudanar da irin Wannan tallafin.

Baba Yawale ya bukaci Waɗanda Suka ci gajiyar tallafin da su Mai da hankali wajen gudanar da sana’o’in da aka kowa musu ,Sannan ya gargadesu dasu guji sayar da Kayan da aka basu Wanda yace hakan ba Abu bane Mai kyau.

“Wadannan da muka koyawa sana’o’i mun tabbatar sun Kore kafin mu yayesu, Sannan Kuma kowanne daga Cikin su sai daya dinka kaya Kuma wadannan Kaya su Muka dauka muka Kai yankunan karkara don rabawa marayun da ko Kayan sawa.” Inji Shugaban Gidauniyar

Haka kuma gidauniyar ta sake kaddamar da wasu sabbin wadanda zata kara koyawa sana’o’i su kimanin 500 a Karo na biyu.

Sana’o’iin da take daukar nauyin koyar da matasan sun hada da sana’o’i,ar dinki hada turare hada takalma

Aisha Aliyu da Rukayya Muhd na daga Cikin Matan da suka koyi sana’ar dinki sun Kuma godewa Gidauniyar bisa abun alkhairi da Suka ce anyi musu Wanda Zai inganta Rayuwarsu tare da bada tabbacin zasu yi Aiki da abun da Suka koyan don inganta Rayuwar su data ‘ya’yansu.

Daga karshe an karrama wasu Mutane wadanda suka baiwa gidauniyar gudunmawa ciki kuwa harda bada kyautar ke kunan dinki guda 2 ga wasu dalibai da suka fi kowa kwazo a yayin koyon sana’ar.

12 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...