Ganduje ya kaddamar da Gangamin dashen itatuwa

Date:

Daga Nura Abubakar

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da dashen itatuwa na Shekara ta 2021a Jami’ar Yusuf Mai tama suke dake nan Kano.

Yayin taron Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar Kano da suyi koyi da Wannan kyakykyawar Dabi’ar ta dashen itatuwa don inganta Muhallansu.

Gwamna Ganduje yace dashen itatuwa Yana da matukar muhimmanci ga Rayuwar Al’umma da Kuma inganta muhalli, Inda yace hakan ce tasa gwamnatin jihar Kano ta dawo da dashen itatuwa Wanda aka daina tun Shekarar 1998.

Yace gwamnatinsa ta dauki sha’anin muhalli da muhimmanci hakan tasa ta Kashe kudade Masu tarin yawa wajen tsaftace jihar Kano da inganta muhalli don inganta Rayuwar Al’ummar.

A kokarin mu na ganin mun tsaftace jihar Kano Yanzu haka mun Sanya Hannu Kan yarjejeniya tsakinin gwamnati da Wani kamfani, Kuma inasan Kun shaida irin Aikin da yake wajen tsaftace jihar nan, Ina so ku sani mun Kashe kudade Masu tarin yawa don maganin Matsaloli gurbacewar muhalli.” Inji shi

Gwamnan Ganduje yace ya zama wajibi al’ummar Kano da kungiyoyin da suke da alaka da muhalli dasu marawa yunkurin gwamnati bayan wajen gudanar da dashen itatuwa a yankunasu don inganta muhalli.

” Ina Kira ga Iyayen Kasa Sarakuna Malamai Yan Kasuwa Manoma makiyaya da dukkanin al’ummar jihar Kano daku tabbatar Kun baiwa gwamnatin hadin Kai domin Samun matsala gurbacewar muhalli ba’ inji Ganduje

Da yake jawabin maraba Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano Dr Kabiru Ibrahim Getso yace dashen itatuwa wajibi ne domin Suna Hana kwararowar hamada da dumamar yanayi da ma Magance duk Wasu Matsaloli na muhalli.

Dr Getso yayi Jawabi Mai tsaho Kan Matsalolin da Sare itatuwa tare da bayyana irin kokarin da Gwamnatin Kano karkashin Ma’aikatar Muhalli keyi domin Inganta aiyukan Ma’aikatar domin cigaban Muhalli a jihar Kano.” Inji Dr Getso

14 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...