Da Dumi-Dumi: Lauyoyin Abduljabbar sun ce sun janye daga wakiltar kare shi a Kotu

Date:

A ci gaba da zaman sauraren karar malamin da ake yi, duka lauyoyin Abduljabbar ba su halarci zaman kotun ba na ranar Alhamis.

Wakilin BBC da ya halarci zaman kotun ya ce lauyan Abduljabbar daya ne ya je kotun Barista Haruna Magashi kuma take ya ce ya janye daga wakiltar malamin.

Ya kuma ce “Sauran lauyoyin su ma sun janye daga kare Abduljabbar shi ya sa dukkansu babu wanda ya halarci zaman kotun.

A bayanin sakamakon gwajin asibitocin da aka gabatar wa kotun, Asibitin Dawanau na masu matsalar kwakwalwa ya ce an taɓa kwantar da Abduljabbar a asibitin na tsawon kwana hudu a baya.

“Lokacin da ya fara yin rikici da ‘yan uwansa an taɓa kwantar da shi a asibitin na kwana hudu, amma ba a taba yi masa gwaji ba kuma ba a taba ba shi magani ba,” in ji mai karanto bayani a gaban kotun.

Alkali Ibrahim Sarki Yola wanda ke yin shari’ar, ya tambayi sakamakon Asibitin Murtala da aka kai Abduljabbar domin yi masa gwajin kunne, saboda gaza amsa tambayoyin da aka yi masa a zaman kotun na baya, wanda ake tsammanin ko ya samu matsalar kunne ne.

“A sakamakon gwajin kunnen da muka samu daga Asibitin Murtala, an tabbatar da cewa Abduljabbar ba shi da matsalar kunne ko kuma ji ko kadan,” mai gabatar da bayani ya ce.

Alƙali Yola ya ce ya amince da buƙatar lauyoyin Abduljabbar na janye wa daga kare malamin.

An dage sauraren karar Malamin zuwa ranar 30 ga watan Satumbar 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...