An Kaddamar da Jami’an Hisbah nasa kai su 477

Date:

Daga Barira Jamil Isa

A Ranar talatar nan ne aka kaddamar da Jami’an sa kai na Hisaba Wato Hisba Marshall a Kano domin. Tallafawa kokarin Hukumar na Hana aiyukan badala a Kano.

Yayin Kaddamar da Jami’an Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano Dr. Muhammad Sani Ibn Sina, ya hori Yan Hisbah Marshall dasu Mai da hanhakali kan aikin su don Magance aiyukan badala a Kano.

Ibn Sina ya Kara da cewa dokar Jihar Kano ta shekarar 2003, itace ta samar da Hukumar Hisbah domin kawar da mummuna da dabaka kyakykyawa.

Da yake nasa jawabin Darakta Janar na Hukumar Hisbah Dr. Aliyu Musa Aliyu, yace wadannan sune kashin farko da sabbin Jami’an Hisaba na sa kai zasu fara gudanar da aiki su a shelkwatar Hisbah, ya kuma hore su dasu zama masu gaskiya da Rikon Amana.

Wasu daga cikin Jami’an Hisbah Marshall sunce sun jima suna so su bayar da gudun mawarsu wajen taimakawa aikin Hisbah, wajen kawar da aiyukan badala da kuma jaddada kyakykyawan aiki a jihar Kano Baki daya.

Kadaura24 ta rawaito cewa sabbin Jami’an Hisabar zasu fara aikin be a Shalkwatar dake Sharada a cikin birnin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...