Da dumi-dumi: Buhari ya Sauke Sanata Lado daga Shugabancin NAPTIP

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke Sanata Basheer Mohammed Lado Daga kujerar Darakta Janar na hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP).

An sauke Mohammed Lado ne kasa da watanni hudu bayan ya karbi ragamar hukumar.

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Kafafen Yada Labarai, Garba Shehu, ya ce shugaban ya amince da nadin Fatima Waziri-Azi a matsayin wanda zata maye gurbin Sanata Lado.

Garba Shehu ya ce nadin ya biyo bayan shawarar da ministar kula da ayyukan jin kai da kula da bala’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayar.

Kadaura24 ta rawaito an musanyawa Mohammed Lado mukaminsa na Babban Kwamishinan a Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira zuwa Hukumar Naptip Kasa da watanni 4 da Suka gabata.

17 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...