Kotun Shari’ar Musulunci dake Zamanta a Kofar kudu karkashin jagorancin Mai shari’a Malam Ibrahim Sarki Yola ta bada Umarnin Kai sheikh Abduljabar Kabara asibitin Dawanau domin duba Lafiyar kwakwalwarsa.
Yayin Zaman kotun na Wannan Rana Bayan kotun da bada Umarnin a karatowar Abduljabar laifukan da ake tuhumarsa ,Amma Abduljabar da lauyoyinsa basu ce komai ba game da tuhumar.
Kadaura24 ta rawaito Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya bada Umarnin a rubuta kwafin shari’ar Baki daya a baiwa lauyoyin Abduljabar din nan take ba tare da bata Lokaci ba.
Mai shari’a Sarki Yola yace Koda lauyoyin Abduljabar sun ɗaukaka Kara hakan bazai hana cigaba da shari’ar ba.
Saraki Yola ya dage Zaman zuwa Ranar 19 ga Wannan Wata na satumba da muke ciki domin cigaba da shari’ar
Allah yakara daukaka wannan gida na kadaura 24 domin munajin dadin kasan cewa da gidan jaridar kadaura24 masha Allah