Matsalar tsaro: Tambuwal yasa Sabbi Dokoki a Sokoto

Date:

GWAMNATIN JIHAR SOKOTO TA KAFA SABBIN DOKOKI DON YAKI DA RASHIN TSARO A FADIN JIHAR SOKOTO.

Gwamna Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal na jahar Sokoto ya aminta da kafa dokoki domin ganin an magance matsalar tsaro a wasu yankunan jahar Sokoto dake fama da Yan Ta’adda Ga dokokin kamar haka;

1- An Haramta Bi hanyar Marnona Zuwa karamar Hukumar Isah har sai baba tagani daga yau. A Don haka ake ba matafiya da ababen hawa shawara da subi hanyar Goronyo-SabonBirni-Isah

2- An haramtawa Manyan motoci/ Sauran ababen hawa masu daukar itacen girki shiga dajin Daga yau.

3- An haramta siyarda kowacce irin dabba a kasuwannin kananan hukumomin Gada, Goronyo,Gudu, Illela, Isa, Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal,Tangaza, Tureta, da Wurno.

4-An haramta daukar Dabbobi da manyan motoci da sauran ababen hawa a kananan hukumomin Gada, Goronyo,Gudu, Illela,Isa, Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal ,Tangaza, Tureta, da Wurno.

5- An haramta daukar mutum uku akan Babur daya da kuma fiyeda mutum 3 a mashin mai kafa 3 (Agwagwa).

6- An haramta siyarda tsoffin babura ko kuma wadanda aka taba amfani dasu a kananan hukumomin Gada, Goronyo,Gudu, Illela,Isa, Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal ,Tangaza, Tureta, da Wurno

7- An haramta amfani da Babur da kuma Keke-Napep daga 10pm na dare zuwa karfe 6am na safe a cikin babban birnin jaha, haka ma an haramta hakan daga karfe 6pm na yamma zuwa 6am na safe a kananan hukumomin Gada, Goronyo,Gudu, Illela Isa, Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal,Tangaza, Tureta, da Wurno.

8- An haramta siyarda Man petrol ga yan bunburutu (Black Markets) Ko kuma siyar musu a gidajen mai.

9- Gidajen mai kadai da aka aminta dasu zasu siyarda man Fetur da diesel Wanda bai wuce Naira 5,000 ba a kananan hukumomin Gada, Goronyo,Gudu, Illela Isa, Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal,Tangaza, Tureta, da Wurno.

10- Maaikatan da kadai zasu iya amfani da babura da keke-napep a lokacin dokar sune MAAIKATAN LAFIYA, JAMI’AN TSARO, YAN JARIDA.

114 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...