Zakirin Shekara : An bukaci Gwamnatin tarayya ta Samar da Hanyoyin da talakawa zasu Sami Saukin Rayuwa

Date:

JAWABIN BAYAN TARON ZIKIRIN JUMA’A DA YIWA KASA ADDU’A WANDA MAJALISAR SHURA TA DARIQAR TIJJANIYYA TA SABA YI DUK SHEKARA A FADAR MAI MARTABA SARKIN KANO, ALH. AMINU ADO BAYERO WANDA AKA GUDA AR A RANAR JUMA’A 18TH GA MUHARRAM 1443 (27TH AUGUST, 2021) .

A ranar Juma’a ne, 18 ga Muharram 1443 wanda ya dai dai da 27 ga Agusta 2021 Majlisar Shura ta Darikar Tijjaniyya, ta shirya taron Zikiri da yiwa Kasa Addu’a, karo na Ashirin da Uku (23). Taron ya gabatar da Zikiri da Addu’a ta musamman domin samun dawwamammen zaman lafiya a cikin kasar mu Nijeriya tare da neman sauki a wajen Allah na mawuyacin halin da al’umma suke ciki.

Taron Mai Taken “Samun tsaro da sassauta kunchin rayuwa ga Al’umma.” an gabatar da shi ne a fadar Maimartaba Sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Bayero kamar yadda aka saba.

Cikin Wata sanarwa da Sakataren yada labaran Kwamitin taron Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa Kadaura24 yace taron ya samu nasarar halartar Shugabannin Gwamnati, Sarakuna, Yan kasuwa, Shehunnai, Muqaddaman Darikar Tijjaniyya da kunzumin al’ummar Musulmi daga sassa daban daban na kasar nan da makwabtan ta.

A karshe Taron ya cimma matsaya kan al’amura kamar haka:

1. Taron ya yabawa Jami’an Tsaro wajen kokarin su na takura masu tada kayar baya na Arewa maso Gabashin kasar nan, a inda suka fara mika wuya ga hukumomi.

2. Taron ya yabawa Gwamnatin Jihar Kano abisa kokarin da take yi wajen dakile wani Baragurbin Malami da yake yada mummunar fahimtar sa ta yin suka ga Janibin Annabi Muhammadu (S.A.W), Iyalin gidan sa da Sahabban Sa.

3. Taron yana kara yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa kokarin ta wajen shirya Addu’oi na musamman da tallafawa harkar tsaro don samar da dorewar zaman lafiya a jihar Kano.

4. Taron ya yabawa Masarautar Kano wajen Jajircewar ta, goyon baya da tallafawa domin tabbatar da dorewar wannan taron duk shekara.

5. Taron yana kira ga Gwamnatin tarayya da ta kara duba wajen gyaran hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasa don a sawwaka wa yan kasa halin da suke ciki na kunci , mastsi, talauci da wahalhalun rayuwa.

6. Taron yana kira ga Gwamnati tarayya da ta kara damara wajen yaki da cin hanci da rashawa da kawo karshen yin garkuwa da mutane, Kisan gilla, Fashi da makami, amfani da miyagun kwayoyi da shauran munanan dabi’u don samar da al’umma ta gari.

7. Muna kira ga Gwamnatin tarayya ta tabbatar ta kama mutanen da suka yiwa wasu musulmi kisan gilla a garin Jos da yi musu hukunci kamar yadda doka ta tanada.

8. Taron ya ja hankalin mahalarta akan su zabura wajen neman Ilmi, aiki da shi da kaucewa san girma a wajen rayuwar mu ta yau da kullum.

9. Taron ya yi kira ga Jama’a da su cigaba da rike kyakkyawan tafarkin magabata tare da kokarin gadar da wannan aiki ga yarn mu masu tasowa.

10. Taron ya zaburar da mabiya akan riko da Darika tare da kulawa da Yanuwantaka ta musulunci.

11 Taron ya yi Janhankali akan riko da ladubban Darika da kiyaye hakkin yan uwa da kaucewa cutar da juna ta hanyar Algus, tauye mudu, saba alkawari, hana Zakka don samun wadata da habakar tattalin arziki da samun zaman lafiya.

12. Taron yayi kira ga shugabanni da su yi Adalci don kyautata rayuwar al’umma tare da kira ga al’umma da su guji zagi da tsinuwa ga Shugabanni don kaucewa tabarbarewar rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...