AMBALIYAR RUWA A KANO: sama da gidaje 1,000 sun rushe, mutane 23 suka rasu – Sale Jili

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA ta ce gidaje sama da dubu daya (1,000) ne suka rushe a kananan hukumomi shidi 6 a nan Kano tunda damuna ta fadi zuwa yanzu.

Shugaban hukumar Alhaji Sale Jili ne ya bayyana hakan a tattaunwarsa da wakilin Kadaura24 a Kano.

Ya ce daga faduwar damuna zuwa yanzu mutane 23 suka rasu, wasu 11 suka jikkata yayin da gidaje dubu daya da talatin da biyar (1,035) suka rushe a kananan hukumomi shida 6 da ke jihar.

Ya ce a hukumance, kananan hukumomin da aka samu ambaliyar sun hada da Bunkure da Rano da Minjibir da Tsanyawa da Doguwa da kuma Tarauni.

“A Bunkure ruwan farko da akayi gidaje 250 suka rushe sannan a akayi wani ruwan gidaje 184 suka rushe, mutane 6 suka jikkata inda kiyasin asarar ya Kai sama da naira miliyan 36. A Rano gidaje 150 suka rushe da kiyasin asarar ya Kai sama da naira miliyan 11. A Minjibir kuwa mutane 4 suka mutu wasu 5 sukaji raunuka yayin da gidaje 272 suka rushe. A Tsanyawa mutane 108 suka rushe yayin da a Tarauni gidaje 67 sai kuma Karamar hukumar Doguwa da mutane 18 suka rasu,”

Shugaban hukumar ya ce idan zaa iya tunawa a shekarar da ta gabata dukkan mazabu 484 na kananan hukumomi 44 sai da aka samu ambaliyar ruwa inda ya ce idan aka ki daukar matakai tarihi zai iya maimaita kansa.

“A bara, hukumar hasashen yanayi ta tarayya ta yi hasashen cewa zaa iya samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 20 cikin 44 dake nan Kano, amma da akayi rashin saa kowacce karamar hukuma sai da aka samu, to bana kuma hasashen ya nuna cewa kananan hukumomi 25 ne, to me kake tunanin zai faru?, hakan ya nuna dole sai mun zage damtse domin rage barnar da ka iya haifarwa sanadiyyar Ambaliyar ruwan”.

Alhaji Sale Jili daga nan ya bukaci alumma musamman a kananan hukumomin Birni da kewaye da kuma Ungogo wanda aka ce sune zai iya fin shafa da su guji zuba shara a magudanan ruwa inda ya bukaci mawada dasu rika agazawa yunkurin gwamnatin jihar Kano na tallafawa wandanda wani iftila’I ya shafa domin rage musu radadin halin da suka samu kansu a cikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...