Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Sarkin Kano da aka sauke kuma Khalifan Tijjaniya, Malam Muhammadu Sanusi II, a karon farko ya yi magana game da cire shi da akai akan gadan sarautar Kano yana mai cewa da gangan ya yanke shawarar ya bar sarautar.
Khalifa Sanusi II wanda ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa a ranar 31 ga Yuli, Inda ya Cika Shekaru 60 ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da Jaridar THISDAY.
Khalifa Sanusi ya ce a cikin hirar, “Na kalubalanci gwamnatin jihar Kano akan ciyo bashin $ 1.8bn Wanda tace zata yi aikin layin dogo dasu, duk da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, rashin abinci mai gina jiki da karancin Kayan more Rayuwa da muke da su.
“Na kuma yi kira da a gudanar da sahihin zabe kuma na shawarci jama’a da su zabi shugabanni masu gaskiya da kishin kasa wadanda suka cancanta”. Inji Sanusi
“A wurina, aikina ne a matsayin Sarki in Yi Magana akan abun da zai kawowa Jama’a cigaba, amma ban sani ba ko wadannane abubuwan da suka haifar da cireni ” kamar yadda kuka ce, amma na san cewa babu wanda zai iya tserewa kaddarar Allah. Lokacin da Allah ya ce lokacin ku ya kare to ya kare din. ”
“Rashin yin abin da na yi imani da shi ba zai taba iya sa na kara kwana ko daya a kan kujerar ba fiye da yadda Allah ya kaddara min. Idan ranar ta zo, zan bar kujerar a mace ko a raye.
Khalifa ya ci gaba da cewa, “Duk maganganun da nayi Ina sane, kawai na yanke Shawarar yin hakan ne da gangan don na bar mukamin da nake Kai cikin mutunci da koma ,a ganina gwara na bari Cikin mutunci da na zauna akan kujerar babu mutunci Kuma an wulakantani.
“Zabi ne da na yi ina sane, Ina alfahari da kaina kuma ina farin ciki da Matakin dana dauka. Kuma, Allah ya kara ɗaukaka ni ya bani Matsayi fiye Dana baya.. ” inji Khalifa Sanusi
Da yake amsa tambaya a kan hanyar da yake bi wajen sokar gwamnatoci, Khalifa ya ce, “Lokacin da nake ‘Sarkin ina da cikakkiyar masaniyar raunin matsayina, Amma ban daina ba. A ko da yaushe ina cewa idan a matsayin ka na Basarake yi shiru a lokacin da ake buƙatar ka yi magana kan Wani abun Daya Shafi al’umma kayi shiru saboda tsoron damar yan siyasa, to babu shakka baka Zama Sarki ba kawai ka Zama bawa ne da Kayan Sarki. ”
A watan Maris na 2020 ne gwamnatin jihar Kano ta sauke Muhammadu Sanusi daga mukaminsa na Sarkin Kano saboda zarginsa da “rashin biyayya” ga Gwamnati, da kuma yin abubun da basu dace ba.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya ce an cire sarkin ne “domin kare martabar al’ada, addini da martabar masarautar Kano da aka ginata sama da shekaru dubu da suka gabata.