Kotu taki Amincewa da bukatar Abduljabar na ajiye shawarwarin Shugaban Mukabala

Date:

Babbar Kotun Jihar Kano da Babban Mai Shari’a, Justice Nura Sagir ya jagoranta ta ki amincewa ta ajiye shawarwarin Farfesa Salisu Wanda ya Shugabanci Zaman mukabalar tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu Malaman Musulunci a Kano da aka gudanar a jihar a ranar 10 ga Yuli, 2021.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Sagir ya tabbatar da cewa Abduljabbar ya zabi halartar mukabalar da kansa inda ya ce ba a tursasa shi zuwa wurin taron ba.

Ya kuma ce Muqabalar ba Shari’a ba ce kuma kotu tana da ikon rushewa ko yin bita kan Shawarwarin da aka gabatar yayin mukabalar, yana mai jaddada cewa mukabalar lamarine daya Shafi ma’abota Ilimi Kuma akan shiryata ne tsakanin malaman da suke da ra’ayi daban -daban .

Mai shari’a Sagir ya ci gaba da cewa Abduljabbar ya amince da sharuddan Mukabalar a martanin da ya mayarwa Gwamnan Kano likacin da aka gayyace shi, Don haka ya ki amincewa ya sake yin nazari tare da soke hukuncin da shawarwarin da Farfesa Salisu Shehu ya bayar.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa lauyan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, Barista Saleh Muhd ​​Bakaro ya roki kotun ta soke hukunci da shawarwarin Farfesa Shehu Shugaban Mukabalar da akai da Abduljabar da Wasu Malamai a Kano Saboda abun da ya kirawo Rashin baiwa Wanda yake karewa ishashshiya damar Kare kansa.

185 COMMENTS

  1. Wannan jaridar taku bantaba Karo da itaba,amma yanzu na ganta kuma ta burgeni nagode Allah ya kareta daga dukkan abinki.

  2. Британский боксер-тяжеловес Энтони Джошуа оценил силу своего следующего соперника, украинца Александра Усика. По его мнению, бой получится сложным. Джошуа готовит себя к 12 раундам. При этом британец заявил, что Джошуа Усик дивитися онлайн Бой Усик-Джошуа – коэффициенты букмекеров

  3. Усик – Джошуа: 7 речей, які об’єднують боксерів. Непросте дитинство загартувало спортсменів, які забезпечили безбідне життя своїм матерям Джошуа Усик смотреть онлайн Дата бою Усик — Джошуа. Про те, що зустріч двох супертяжів відбудеться 25 вересня, було оголошено в липні. 13 липня генеральний директор компанії К2 Promotions Олександр Красюк заявив, що сторони досягли попередньої

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba gaskiya a bayanin wasu Manoman Kano da suka ce Muna karbar kudi a wajensu – Civil defense

Rundunar tsaro ta Civil defense ta Kasa reshen jihar...

Korar ma’aikata a Kano: Bashir Gentile ya yiwa Faizu Alfindiki martani mai zafi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi...

Sakataren kungiyar NRO Abdulkadir Gude ya rasu

Allah ya yi wa dattijo, kuma Sakataren kungiyar Northern...

Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki

Daga  Maryam Muhammad Ibrahim   Abin takaici ne ganin yadda gwamnatin...