Bikin Cika Shekaru 60: Khalifa Sanusi II ya biya Sama da Naira Miliyan 20 don fitar da Wasu Daga gidan yari

Date:

Daga Rabi’u Usman

Mai Martaba Sarkin Kano na 14 Kuma Khalifan Tijjaniyya na Nigeria Malam Muhammad Sunusi ll ya fitar da Wasu Mutane daga Gidan Ajiya da Gyaran Hali a Nan Kano Kimanin Mutane 38, Duk dai A Cikin Bikin Cikar Sa Shekaru 60 a Duniya.

A Gidan Ajiya da Gyaran Hali na Kurmawa Kimanin Maza 14 ya Biya Musu Bashi da ake Binsu da Kuma Tarar da Akayi Musu Kimanin Naira Miliyan 17, da Dubu 779. Sai Kuma Gidan Ajiya da Gyaran Hali na Goron Dutse ya Biya wa Mutane 24, daga Cikin Su akwai Mata 4 da Maza 20, Naira Miliyan 7,da Dubu 186, Wanda Jimullar Adadin kudin Sun Tasamma Naira Miliyan 21,779,600.

Jim Kadan da Fitowa ne Muka Zanta da Wakilin Muhammad Sunusi na ll, Mujitaba Abubakar Abba (Falaki Mai Kada), inda ya Bayyana mana Cewar, Duk wanda yasan Sunusi na ll, yasan yana Gudanar da irin Wannan Taimakon ta Kowacce fuska, ya Kara da Cewar Lallai babu Shakka Za Suci gaba da Gudanar da Aikin Alkhairin nan Kamar yanda Addinin Musulunci ya Bada Umarnin ayi.

Guda Daga Cikin Alkalan Kotun Majistare a Nan Kano Mai Shari’ah Salisu Idris Sallama ya Bayyana Godiyar Su Dangane da Wannan Abin Alkhairi daya Wakana a Jihar Kano a Madadin Ma’aikatar Shari’ah ta Jihar, Wanda Kuma Shi ne Alkalin da ya yanke Hukunci ga Guda Daga Cikin Wadanda Suka Shaki Iskar’yanci a Wannan Rana aka Biya Masa Zunzurutun Kudi Naira Miliyan 6.

A Karshe dai Wakilin Kadaura24 Rabi’u Usman ya Ruwaito Mana Cewar, daga Cikin Wadanda Suka Shaki Iskar yanci sun Hadar da Musulmi da Wanda ba Musulmi ba Kuma duk sun godewa Khalifan Saboda kokarin da yayi na fitar dasu Daga wancan gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...