Daga Sadeeq Y Sadeeq
A Wani wasan sada zumunci da kungiyar kwallon kafa ta Hukumar Gidan gyaran Hali ta Kasa reshen jihar Kano wato (Kano Correctional Tigers) ta fafata da takwararta ta hadakar Rundunar Yansan ta kasa dake Garin Wudil.
Wannan bayani na kunshe ne Cikin Wata sanarwa da Shugaban Yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Hukumar lura da Gidajen gyaran hali ta kasa reshen jihar Kano Abbas A Musa ya Sanya Hannu Kuma aikowa Kadaura24.
Sanarwar tace wasan Kungiyar Kwallon Kafa ta hadakar Rundunar yan’sanda ta kasa dake garin wudil ta ci daya yayin da takwararta ta Hukumar Gidan Gyaran Hali wato (Kano Correctional tigers) take nema.
Wannan wasa dai an fafatashi ne a can karamar hukumar wudil da ke nan Kano a Ranar Lahadi da misalin Karfe 4 na yamma.
Sanarwar tace anyi wasan lafiya Kuma an tashi Lafiya ba tare da wata matsala ba.