2023 : Ba zan Nemi kujerar Shugaban Kasa ko Mataimaki ba – Ganduje

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa a Shekara ta 2023 Bai gayawa kowa Zai nemi kujerar Shugaban Kasa ko Mataimakin Shugaban Kasar nan ba.

Kadaura24 ta rawaito Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne Yayin Wata Hira da yayi da Gidan Radio Nagarta dake jihar Kaduna a safiyar Larabar nan.

Ganduje yace bashi da wata niyya ta Neman Waɗancan kujeru kamar yadda Wasu ke yadawa cewa Yana neman kujerar Shugaban Kasa ko Mataimakin Shugaban Kasa.

” Sau tari Waɗanda Suka damu ko Suka nuna kwalamarsu wajen nema Wata kujera a Kasar nan basu Cika Samun Nasara ba” inji Ganduje

Yace shi burinsa ya kammala mulkin jihar Kano lami lafiya ya Sami Wanda Zai gajeshi Wanda Zai Mai da hankali wajen kawowa Kano cigaba dai-dai gwargwado.

“Zamu duk Mai yiwuwa wajen ganin mun Magance yan Matsalolin da muke dasu ta Hanyar masalaha tunda dama ita Siyasa ai masalahace, Kuma da yake ma ni ba talakamin karfe gareni ba ,ni talakamina na cike yake da soso ta yadda ko na taka Mutum ba Zai sanma na taka shi ba”. Inji Gwamna Ganduje

Idan Mai karatu Zai tuna yasha Jin ana cewa Ganduje Yana Neman Shugaban Kasa ko Mataimakin Shugaban Kasa Idan ya kammala wa’adin Mulkin Kano.

162 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...