Daga Zubaida A Ahmad
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu na kimanin Naira miliyan sama da Naira Miliyan 10 sakamakon gobarar da ta afku a wasu sassan jihar a watan da ya gabata na Yuli.
Kadaura24 ta rawaito Saminu Yusuf Abdullahi Jami’in hulɗa da Jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa Daya fitar.
Sanarwar ta ce Hukumar a karkashin jagorancin Alhaji Hassan Ahmad Muhammmad a cikin watan da ya gabata na Yuli 2021, ta samu kiran gaggawa daga tashoshin kashe gobara har 27 da ke fadin jihar.
A cewar sanarwar, Hukumar ta karbi kiran wuta 32, da Kira na ceto 64, sai kiran Karya 21.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An kiyasta kadarorin da gobarar ta lalata N10,500,000, An kiyasta kadarorin da aka tseratar N27,900,000, an rasa rayukan Mutane 11, tare da Ceto rayuka 107”.
A cikin sanarwar, Hukumar Kashe Gobara ta umarci jama’a da su rika kula da wuta don gujewa tashin gobara.
Ya kuma umarci jama’a da su rika bin dokokin Hanyoyin don gujewa hatsari tare da yin kira ga Iyayen yara da su Rika sanya ido kan ‘ya’yansu don Gudun Wasa a kududufi a unguwannin su.
Sorry