Zamu kashe sama da miliyan 160 wajen gina ofishin ‘yan sanda a Gwarzo- Dr Kabiru Getso

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata kashe sama da naira miliyan 160 wajen Gina ofishin ‘yan sanda a Garin Getso cikin karamar hukumar Gwarzo.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin da ya kaddamar da aza harsashin ginin a tsohuwar tashar motar garin na Getso.

Kwamishinan ya ce zaa Gina babban ofishin ‘yan sanda kamar na kowacce Karamar hukumar, Kuma a cikinta zaa samar da gidan babban baturen ‘yan sanda da gidajen manya da kananan ‘yan sanda da za suyi aiki a ofishin cikin harda dogon ginin hangen nesa Wanda zai bawa jami’an ‘yan sanda damar gano mutane daga nesa.

Ya ce Sabon ofishin’yan sandan zai tallafawa Wanda ake da shi yanzu a Mazabar Gwarzo Kuma zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar mazabu 10 da ke yankin karamar hukumar ta Gwarzo.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce ana sa ran zaa kammala aikin a watanni 8 masu zuwa kuma ana sa ran gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne zai bude shi idan an kammala.

“Wannan bangare na yankin karamar hukumar Gwarzo mun fuskanci matsalar tsaro a baya, Muna da mazabu 10 a nan, saboda haka idan ka duba samar da wannan ofishin zai taimaka wajen samar da Karin jami’an tsaro da kuma kayan aiki” Getso ya ce.

“Wannan Sabon ofishin ‘yan sandan da zaa gina ba wai zai kula da tsaron mutanen Getso kawai ba ne, zai kula da rayuka da dukiyoyin al’ummar mazabu 10 na Gwarzo” inji Dakta Kabiru Getso,” inji Getso.

Kwamishinan ya kuma ce za’a samar da sabon guri a nan gaba kadan za za’a mayar da tashar motar da aka tasa inda ya ce anyi hakan ne domin tabbatar da tsaro Kuma tsaro a gaba da komai ya ke.

A jawabinsa yayin taron, San Getso Alhaji Bello Ibrahim Getso ya bukaci masu amfani da kafofin sada zumunta da su guji fakewa da siyasa wajen cin mutuncin mutane a kafafen sada zumunta, Yana Mai cewa idan baa dauki mataki ba hakan zai iya kawo tashe-tashen hankula a tsakanin al’umma.

Bello Ibrahim Getso daga nan ya bada tabbacin hadin kan al’ummar yankin domin cimma nasarar da aka sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...