Zargin Rashawa: EFCC ta kama tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura da matarsa

Date:

Hukumar EFCC a Najeriya ta kama tsohon gwamnan Nasarawa kuma sanata a yanzu Umaru Tanko Al-Makura da matarsa kan rashawa.

Jaridar Premium Times a Najeriyar ta rawaito cewa yanzu haka ana riƙe da tsohon gwamnan da matarsa a ofishin EFCC da ke Abuja.

Jaridar ta ce duk da cewa babu wasu cikakkun bayanai, majiyoyi na tabbatar da cewa kamen na da alaƙa da rashawa da aka tafka a mulkin shekara 8 da ya yi na gwamna a Nasarawa.

Al-Makura ya jagoranci Nasarawa daga shekara ta 2011 zuwa 2019 kafin daga bisani ya tafi majalisa a matsayin Sanata mai wakiltar Nasarawa ta kudu.

68 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...