Wani Basarake, Dan Kasuwa Kuma Dan kishin Kasa Ambasada Yunusa Yusuf Hamza (Falakin Shinkafi) yace ya Zama wajibi Iyayen yara su San irin Malaman da zasu Rika tura ‘ya’yansu wajensu don neman Ilimin addini Saboda lalacewar Wannan Zamanin.
Amb. Yunusa Yusuf ya bayyana hakan ne lokacin Daya jagoranci taron taya Murnar cikar Wata makaranta Mai Suna Abdullahi Ibn Fodio Shekaru 40 da kafuwa a unguwar Yakasai dake Karamar Hukumar Birnin Kano.
Yace Sabbin al’amuran da suke fitowa Daga Wasu da suke kiran kansu Malamai Kuma suke koyawa Matasa hakan yana gurbata imanin Matasan da Kuma jefa su Cikin ta’addanci da Sunan addini.
” Ku Rika tantance irin Wadancan Malamai Saboda zamani ya lalace, Wasu Malaman kawai Suna hakan ne don son yin suna., ba Wai su koyar da Dalibai abun da Allah da Manzonsa Suka ce ba”. Inji Falakin Shinkafi
Falakin Shinkafi Wanda shi ya zamo Uban taron ya Bukaci al’ummar jihar Kano da Nigeria su zauna lafiya da juna don Samun Cigaba Mai dorewa, Saboda sai da Zaman lafiya ake Samun kowanne irin cigaba.
Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya yabawa Khalifan Darikar Kadiriyya na Africa Sheikh Karibullah Sheikh Nasiru Kabara Saboda girmama gaiyatar da kai Masa ,Sannan ya yabawa Iyaye da Malaman makarantar Wanda yace da ba’a Sami hadin Kai tsakanin Iyaye da Malaman makarantar ba da makarantar Bata Kawo Wannan Lokaci ba.