Majalisar Dokoki ta bukaci Gwamnatin kano data Samar da Wasu tituna a kano

Date:

Daga Kamaluddeen Sani Zango

An yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta hanzarta  kammala titinan da kwalbatocin da suka hada Garko zuwa karamar hukumar Sumaila.


 Majalisar ta yi wannan kiran ne a yayin zaman ta na yau a wani lamari da ya shafi bukatun al’umma cikin gaggawa wanda dan majalisa mai wakiltar Garko Hon Abba Ibrahim Garko ya gabatar.


 Dan Majalisar ya jaddada cewa hanyar idan aka kammalata zata taimaka wajen inganta cigaban tattalin arziki da harkokin Sufurin yankin.


 Kudirin ya samu goyon bayan dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Sumaila kuma mataimakin kakakin majalisar Rt Hon Zubairu Hamza Massu .


 Majalisar ta amince tare da jawo hankalin Gwamnatin Jiha data hanzarta daukar matakan dawo da ‘yan kwangilar da ke aikin da kuma tabbatar da kammaluwar aikin cikin sauri, la’akari da lokacin damina wanda ke zama babbar barazana ga al’ummar yankin.


 A wata sanarwa Darakta yada labaran Majalisar Uba Abdullahi ya fitar yace a wani labarin kuma an gabatar da wani kudiri da dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Gabasawa Hon Salisu Muhd ​​Dan Azumi wanda Rt Hon Isyaku Ali Danja ya karanta a madadinsa a gaban zauren majalisar Inda ya bukaci Majalisar rayi kira ga gwamnatin jihar da ta gina hanya daga Zakirai zuwa Gumawa, Kawo zuwa Garun Danga a karamar hukumar Gabasawa.


 Majalisar ta amince da yin kira ga gwamnatin jihar da ta gudanar da aikin hanyar.

192 COMMENTS

  1. Джошуа-Усик: объявлен состав пар андеркарда Джошуа Усик смотреть онлайн Александр Усик против Энтони Джошуа. Онлайн-трансляция, реакция, прогнозы на бой 25 сентября в Лондоне на стадионе Тоттенхэм. Фото, видео, реакция соцсетей и мнения экспертов

  2. Дата бою Усик — Джошуа. Про те, що зустріч двох супертяжів відбудеться 25 вересня, було оголошено в липні. 13 липня генеральний директор компанії К2 Promotions Олександр Красюк заявив, що сторони досягли попередньої Смотреть онлайн прямую трансляцию боя Энтони Джошуа – Александр Усик 25.09.2021 Бокс Видео бокса Джошуа – Усик: дата боя (25.09.21), свежие новости боя

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...