Bidiyon Dala:Wata kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jaafar Naira dubu dari 8

Date:

Daily Nigerian, wata kafar yada labarai ta yanar gizo da ake bugawa a Najeriya, da mawallafin ta, Jaafar Jaafar, sun roki babbar kotun jihar Kano da ta umarci gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da ya biya Naira miliyan 400 don biyan diyyar bata musu lokaci da kuma kokarin bata musu suna.


 Ganduje, wanda ya gurfanar da duk wadanda ake zargin a kotu, yana neman diyyar bata masa suna, a ranar Talata ya nemi a dakatar da karar ba tare da bayar da wani kwakkwaran dalili ba.
 Idan za’a iya tunawa Jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna gwamnan yana karbar cin hanci daga hannun wani dan kwangila.


 Amma lauyan jaridar Daily Nigerian, Muhammad Dan’Azumi, ya fadawa kotun cewa gwamnan ya bata lokacin Waɗanda yayi kara da kuma kokarin lalata mutuncin ta da cewa ta wallafa abubuwan batanci.  Ya nemi diyyar naira miliyan 300.
 Hakazalika, lauyan Jaafar, U. U. Eteng, ya nemi a ba shi naira miliyan 100.


 Sun kuma bukaci kotun, ta umarci Ganduje da ya gabatar da sanarwar Hakurin kafin daukar duk wani mataki a kan lamarin.


 Mai shari’a S. B. Namalam ya ba Ganduje takardar dakatar da shi, kuma ta umarce shi da ya biya kudin a kan N400,000 ga wadanda ake kara su biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...