Daga Nura Bala Ajingi
Hukumar kashe Gobara da kai agajin gaggawa ta jahar kano ta danganta asarar rayuka da dukiya akan rashin tanadar lambobinta na kiran neman dauki har sai idan iftila’i ya faru.
Babban Daraktan hukumar Alh. Hassan Ahmed Mohd ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai a ofishinsà.
Ya ce kame kamen neman lambar hukumar a lokacin da iftila’i ya faru yana kawo jinkiri wajen kai dauki wadda hakan ke haifar da asarar rayuka da dukiya.
Shugaban ya yi kira ga al’umma da su rika ajiye lambobin hukumar kafin bukatarsu ta zo domin ceton rayukan al’umma da dukiya akan lokaci.
Lambobin da za a nemi hukumar su ne 08098822631 da 07026026400 da kuma 07051246833
Shugaban hukumar kashe gobarar ta jahar kano ya kuma bukaci masu ababan hawa akan titi da su rika baiwa jami’an hukumar hanya a duk lokacin da suka fita kai agajin gaggawa.
Alh. Hassan Ahmed Mohd ya yabawa gwamnatin jahar kano bisa jagorancin gwamna Abdullahi Umar Gandue saboda gagarumar gudummawar da take baiwa hukumar wajen gudanar da aiyukanta.
Daga bisani ya kuma nuna gamsuwarsa bisa yanda jami’an tsaro da al’umar jahar kano suke ba su hadin kai sannan ya godewa wadanda suka yi musu ta’aziyyar jami’ansu biyu da suka rasu tare da jajanta musu dangane da gobarar da ta shafi jami’ansu a gidan mai na Al’ihsan a unguwar sharada.