Tsadar Abinci: Muhuyi Magaji ya gana da Masu shinkafa a Kano

Date:

A yau ne Shugaban hukumar Karbar korafe-korafe da hana ayyukan cin hanci da rashawa ta jahar Kano, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado ya gana da Shugabancin kungiyar masu kamfanonin Sarrafa shinkafa ta kasa reshen jahar Kano, kan yadda za a magance matsalar tsadar shinkafar a jahar Kano.

A yayin zaman Barrister Muhuyi Magaji ya jagoran ta, Shugabancin kungiyar sun koka kan tashin gwauron zabi da dukkanin bangarorin kayan ayyukan su suka yi tare da neman hukumar ta shiga tsakani don samun rangwame daga gwamnatin tarayya.

A karshe Barrister Muhuyi ya basu tabbacin yin iya bakin kokarinsa domin ganin an saukaka wa Jama’a wahalar tsadar kayan abinci musamman ma shinkafa.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito yadda Kayan Abinchi sukai tashin gwauron zabi Musamman a yan kwanakinan.

63 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...

Gwamnatin Kano ta magantu kan Hukuncin kotu na zaben kananan hukumomi

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Kano ta bayyana farin...