Mun rabawa Kungiyoyin aikin gayya Kayan Miliyan 20-Dr Kabir Getso

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kashe Naira miliyan 20 wajen siyan kayayyakin kwashe shara tare da rabasu ga kungiyoyi ayyukan gayya 100.

Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a lokacin da ya jagoran duba aiyukan makon tsaftar Muhallin a nan Kano.

Idan za’a iya tunawa a jiya Asabar ne gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da makon tsaftar Muhallin a yunkurin Gwamnatin sa na yashe Magudanan ruwa domin kare afkuwar ambaliyar ruwa a fadin jihar nan.

Dakta Kabiru Getso ya ce kayayyakin yashe Magudanan ruwa an rabawa kungiyoyin aikin gayya sama 100 Wanda suka fito daga kananan hukumomin kwaryar birnin Kano da nufin tallafawa yunkurin Gwamnatin jihar Kano na yashe Magudanan ruwa.

“Mai girma gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam a jiya Asabar ya kaddamar da muhimman ayyukan guda 3, Gangamin makon tsaftar Muhallin Wanda zaa dauki kwanaki 7 anayi da Gangamin yaki da bahaya a fili da kuma sanya dokar tabaci a kan tsaftar Muhallin da samar da ruwansha inda ya umarci maaikatar samar da ruwansha da maaikatar Muhalli da sauran hukumomin da abin ya shafa dasu hada karfi da karfe domin kawo karshen bahaya a fili”.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce kayayyakin da aka raba sun hada kurar kwashe shara da Addina da Diga da Shebur da kayayyakin kariya Wanda suka hadar da safar hannu da takalmin ruwa da sauran kayayyaki.

“A Unguwar Gini kawai a iya safiyar yau an debe shara sama da mota 15 kuma kamar yadda kuke gani muna cigaba da aikin har sai mun debe dukkan sharar da ke nan wajen”.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya bukaci al’umma da su guji zubar da shara a Magudanan ruwa inda ya ce akwai bukatar Gwamnati da kamfanoni da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran alumma su hada hanu domin yaki da matsalolin Muhalli da nufin kare yaduwar kananan cututtuka a tsakanin al’umma.

184 COMMENTS

  1. Усик Джошуа – смотреть прогноз букмекеров на чемпионский бой 25.09.2021 – Александр Усик проведет бой против Энтони Джошуа – котировки букмекеров Усик – Джошуа: онлайн-трансляція чемпіонського бою Усик Джошуа – смотреть прогноз букмекеров на чемпионский бой 25.09.2021 – Александр Усик проведет бой против Энтони Джошуа – котировки букмекеров

  2. Якщо Джошуа не зможе позбутися Усика до п’ятого чи шостого раунду, то справа дійде до рішення. А якщо бій триватиме всі 12 раундів, то Усик може перемогти рішенням. Щоб пройти всю дистанцію, в Усик – Джошуа: онлайн-трансляція чемпіонського бою Джошуа больше, богаче и авторитетнее Усика, но может

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...