Osinbajo zai zo Kano Ranar 26 ga Wannan Wata

Date:

Daga Surayya Abdullahi Kabara

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo Zai ziyarci jihar Kano domin Bude wasu aiyuka tare da kaddamar da Wasu aiyukan .

Gwamnan ya bayyana hakan ne Yayin taron Majalisar Zartarwar Jihar na Wannan makon Wanda ya gudana a Ranar Juma’ar nan.

Yace Mataimakin Shugaban Kasar Zai zo ne Ranar 26 ga Watannna da muke ciki domin Bude wasu muhimman aiyuka da Gwamnatin Kano ta gudanar.

Gwamna Ganduje yace Aiyukan da Farfesa Yemi Osinbajo Zai bude sun hadar da gadar Dangi dake kan titin Gidan zo sai Cibiyar koyar da sana’o’i ta Dangote, Sannan zai ziyarci Kasuwar Duniya da Tashar tsandaurin ta dala sai Asibitin cutar Daji da Sauran aiyuka da dama.

Gwamna Ganduje ya Mataimakin Shugaban Kasar Zai Kuma kaddar da Wasu aiyukan a nan Kano Wanda gwamnatin jihar Kano zata gudanar.

Gwamnan yace a Ranar Asabar din nan za’a bada sandar girma ga Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji Muhd Kabir Inuwa Sakamakon Rasuwar Marigayi Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila Wanda ya rasu a bara.

74 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...