Makon Tsafta:Zamu Samar da Makewayi 58 a Birnin Kano- Dr Kabir Getso

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Gwamnatin jihar Kano ta ce shirye-shirye sunyi nisa domin gina bandakuna 58 a cikin kwaryar birnin kano da nufin yaki da dabi’ar bahaya a fili.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci bibiyar ayyukan da ake gudanarwa cikin “makon kula da muhalli na shekarar 2021” wanda gwamnan jihar Kano ya kaddamar a baya-bayan nan.

Dakta Kabiru Getso ya ce a binciken da ma’aikatar muhalli ta gudanar ya gano gurare 58 da ake yawan yin bahaya a fili a cikin kwaryar birnin Kano wanda hakan ne ya sa ma’aikatar ta kudiri gina bandakunan da nufin yaki da dabi’ar ta bahaya a fili.

Ya ce ma’aikatar ta bukaci tallafin hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA da hukumar gyaran tituna ta jihar Kano KARMA da kungiyar direbobin tifa da daidaikun mutane da dukkan masu ruwa da tsaki domin tallafawa yunkurin maaikatar na raba jihar Kano da datti.

“Mun Kai ziayara hukumar KNUPDA Kuma shugaban Hukumar ya tabbatar mana da cewa zai amsa bukatar mu na sahalewa a gina guraren bahaya na jamaa tunda kunsan itace hukumar da ke bada izinin gina Nan Kano, Mun bukaci tallafin hukumar KARMA ita ma ta bamu manyan motocin diban shara guda 3 da yau aka fara amfani dasu, saboda haka kenan akwai bukatar dukkan masu ruwa da tsaki Kamar kamfanoni da kungiyoyin aikin gayya su tallafa mana domin gwamnati ka dai ba zata iya ba”, inji Kabiru Getso.

Ya kuma bayyana jindadin sa dangane da yadda al’ummar jihar Kano suke bada gudun mowar tsaftace muhallansu inda ya ce hakan zai tallafa wajen kare afkuwar ambaliyar ruwa.

Kwamishinan muhallin Dakta Kabiru Getso ya bukaci al’ummar jihar Kano dasu guji zuba shara ko kayan gini ko kuma yin ginin a kan magudanan ruwa inda ya ce hakan yana da matukar hadari ga rayuwar al’umma.

A wani labarin Kuma Hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA ta ce zata rushe dukkan gine-ginen da akayi a Magudanan ruwa a nan Kano.

Shugaban Hukumar Suleiman Ahmad Abdulwahab ne ya bayyana hakan lokacin da yake kabar bakuncin kwamishinan Muhalli na jihar Kano a ofiahinsa.

Ahmad Abdulwahab ya bayyana hakan ne biyo bayan korafin da kwamishinan Muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya Kai masa Kai yadda wasu mutane suke gina wasu guraren Sanaa a kan hanyar ruwa musamman a Unguwar jakara cikin karamar hukumar Birni da kewaye.

Ya ce gini ko ya kai hawa 10 matukar akayi shi ba bisa ka’idaba ko akayi shi akan Magudanan ruwa to doka ta bawa Hukumar damar rushe shi.

56 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...