Adam A Zango ya sake komawa APC

Date:

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya koma bangaren jam’iyya mai mulki ta APC a Najeriya.

Jarumin na Kannywood da ke arewacin Najeriya, ya wallafa komen da ya yi ne a shafinsa na Instagram a ranar Talata inda aka gan shi tare da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

“Kowa ya bar gida, gida ya bar shi.” Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram dauke da hotuna da wani bidiyo da ya nuna shi tare da Gwamna Bello.

“Ga Adamu Zango a nan, muna maka barka da zuwa, ga shi sun dawo gida.” Gwamna Bello ya ce a cikin bidiyon mai tsawon dakika 29.

Gabanin zaben 2019, Zango ya sauya sheka ya koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP, inda har ya gana da dan takarar shugaban kasar jam’iyyar Atiku Abubakar, ya kuma nuna magoya bayansa su zabe shi.

216 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...